Abeokuta

Abeokuta Birni ne, da ke a jihar Ogun, a ƙasar Najeriya. Shi ne babban birnin jihar Ogun. Birnin na nan a kudancin rafin Ogun, a wani yanki dake da duwatsu da manyan itace na Savanna. Birnin na da nisan kilomitoci 77 (48 mi) daga arewacin Legas ta titin jirgin kasa, ko kuma nisa 130km (81 mi) ta ruwa. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2006, jimillar mutane 451,607 ne.


Developed by StudentB