Al-Ghazali | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Tus (en) , 1058 |
ƙasa | Seljuk Empire (en) |
Mazauni |
Nishapur (en) Bagdaza Damascus Jerusalem |
Mutuwa | Tus (en) , 19 Disamba 1111 |
Makwanci | Mashhad |
Ƴan uwa | |
Ahali | Ahmad Ghazali (en) |
Karatu | |
Harsuna |
Farisawa Larabci |
Malamai |
Al-Juwayni (en) Abu Ali Farmadi |
Ɗalibai |
view
|
Sana'a | |
Sana'a | mai falsafa, mutakallim (en) , autobiographer (en) , maiwaƙe, Islamic jurist (en) , journal editor (en) da ɗan jarida |
Wurin aiki | Siriya |
Employers | Al-Nizamiyya of Baghdad (en) |
Muhimman ayyuka |
The Alchemy of Happiness (en) The Incoherence of the Philosophers (en) The Revival of the Religious Sciences (en) |
Imani | |
Addini |
Musulunci Mabiya Sunnah Sufiyya Ash'ari (en) |
Imam Al-Ghazali (furucci|ˈɡɑː|zɑː|li;[1] cikakken sunansa Abū Ḥāmid Muḥammad dan Muḥammad al-Ghazālī da Larabci أبو حامد محمد بن محمد الغزالي; latinized Algazelus ko Algazel, ya rasu a 19 ga watan Disamban shekara ta 1111) ya kasance ɗaya daga cikin shahararru kuma mafi tasiri acikin masana falsafa, tauhidi, shari'a, kuma sufi.[2][3] a cikin mabiya Sunnah.[4] Ɗan asalin ƙasar Farisa ne.[5][6][7]
A al'adar musulunci ana ganinsa a matsayin wani Mujaddadi, wato wanda ya jaddada addini, wanda kamar yadda hadisin Manzon Allah (SAW) ya tabbatar, cewa, "Allah na turo wasu a duk bayan shekara 100 wato ƙarni ɗaya domin su sake jaddada addini dan al'ummah a bayan ƙasa" ("a ƙasashen musulmi").[8][9][10] Ayyukan sa sun kasance abin dogaro daga malamai ƴan'uwansa, Imam al-Ghazali an basa girmamawa da laƙabin "Shaidan Musulunci" (Hujjat al-Islam).[11]
Al-Ghazali ya Kuma yi imanin cewa al'adar addinin musulunci tsakanin musulmai tana dishewa, kuma hakane yasa kimiyyar bautan Allah kamar yadda malaman farko suka karantar da musulmai da su aka manta da su.[12] Hakane yayi Sakamakon yin rubutun sa na magnum opus mai lakabi da Ihya 'ulum al-din ("The Revival of the Religious Sciences").[13] daga cikin wasu ayyukan sa, akwai, Tahāfut al-Falāsifa.