Badarawa

Badarawa, Babban anguwa ce dake Kaduna karkashin karamar hukumar Kaduna ta Arewa. wanda take kewaye da unguwanni kamar haka, daga kudu Unguwan Sarki unguwar rimi, da kuma Unguwan Dosa daga Arewa da Unguwan Kanawa daga yamma (Nigerian Defence Academy), sai Malali daga gabas duk acikin garin Kaduna. Tanada kananan unguwanni kamar su: Kwaru, Malali, Majalisa, Unguwan Yaro, Unguwan Shekara da Unguwan Mai Samari. Duk da Badarawa ta kasu gida biyu ne, birnin Badarwa kamar su Wurno Road, Ogbadu Street da kuma kauyan Badarawa kamar su Kwaru, Majalisa, Ƙaraye Road. Unguwan na da makaranta L.E.A firamare, ana kiranta L.E.A Badarawa 1 da Badarawa 2, inda yaran gari ke gudanar da karatunsu na zamani. A yanzu ta Kara samun habaka na samun gaba da sakandare na jeka ka dawo, wanda akafi saninta da "Day Bola"


Developed by StudentB