Dankali

Dankali da Turanci sweet potato da sunan gona kuma (Ipomoea batatas). Dankali a kan yi masa lakabi da dankalin Hausa kuma ana amfani da shi ta hanyoyi da dama. A kan dafa dankali a ci shi haka nan. Kuma a kan soya shi. Amma dai an fi amfani da shi wajen yin mandako kuma a kan yi amfani da shi wajen yin kunun zaƙi. Yadda ake yin mandako shi ne a kan dafa dankalin sai a bare shi. Bayan an bare sai a hada shi da garin kuli-kuli.


Developed by StudentB