Masallaci

Masallaci jam'i, ko Masallatai: wajene da musulmai ke bautan Allah (SWA) shikadai Ubangijin kowa da kowa. Da Larabci ana cewa Masjid. A wajen akasarin Musulmai, masallaci ya wuce wajen bautan Allah kadai. Musulmai na bauta tareda koyo da koyar da ilimin addinin Musulunci tare da tattaunawa akan matsalolin musulmai tare da neman hanyar warware su a masallaci. A Birtaniya masallatai ne cibiyar matattarar al'umar musulmai tare da koyar da addinin musulunci. Anayin buku-kuwa da taruka a masallaci, musamman ma shagul-gulan daurin aure. Akwai dokokin yadda mutane zasu kasance a masallaci. Daya daga cikin su shine wani bazai takura ma wanda yake bauta ba. Masallatan farko an bude sune a karni na bakwai (7) a fili, amma daga baya an koma ana gina Masallatai a salon gini na Musulunci. Masallatan Quba da masallaci anabi farko farkon masallatai. Akwai masallatai a kowacce Nahiya in banda ta Antarctica.


Developed by StudentB