Yamaltu Deba karamar hukuma ce dake Jihar Gombe, a arewa maso gabashin Najeriya. Tarihin Deba ya fara ne a shekara ta 1375 miladiyya tare da naɗa Sarkin Kuji na farko. Pre-Mishelku, Mishelku, Fulani Jihadi, Mulkin mallaka, da kuma bayan samun ƴancin kai sune tarihin Deba. Ƙaramar Hukumar ta riga ta kasance kafin a kafa Jihar Gombe, amma daga baya ta zama karamar hukuma a cikin Jihar Gombe.[4] Hedikwatar karamar hukumar tana cikin garin Deba ne kuma karamar hukumar na da iyaka da wasu sassan jihohin Borno da Yobe[5]. Yamaltu/Deba. yana da yawan jama'a 255,248.[6] bisa ga ƙidayar jama'a ta shekarar dubu biyu da shida 2006. Mafi yawan mutannen da suke garin Ƴan ƙabilar Tera ne (Terawa), Wanda sauran jama'ah kuma daga wasu ƙabilu mabanbanta.
Developed by StudentB