Shaykh 'Abd al-Raḥman ibn Nāṣir al-Si'dī ( Larabci: الشيخ عبد الرحمن بن ناصر السعدي ), wanda kuma aka fi sani da al-Si'di (1889-1957), malamin addinin Musulunci ne daga Saudiyya.Ya kasance malami kuma marubuci a UnaizahSaudi Arabia. Ya rubuta littafai sama da 40 a fagage daban-daban da suka hada da tafsiri da fiqhu da kuma aqida. al-Sa'di ya kasance mai tasiri a fagen tafsiri kuma littafinsa na tafsiri mai suna Taysir al-Kareem al-Rahman an bayyana shi a matsayin daya daga cikin shahararrun tafsirin malamansalafiyya na zamani.[1] Ya yi aiki a matsayin limami da khateeb namasallacin <i id="mwHA">jami</i>' mafi girma kuma darakta na makarantar horar da addini, al-Ma'had al-'Ilmi, na Unayzah.