Addinan Ibrahimiyya | |
---|---|
religion type (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | monotheistic religion (en) |
Farawa | 2 millennium "BCE" |
Suna saboda | Ibrahim |
Wanda ya samar | Ibrahim |
Has characteristic (en) | monotheism (en) |
Addinin Ibrahim shi ne addini wanda mabiyansa suka yi imani da annabi Ibrahim. Sun yi imani Annabi Ibrahim da 'ya'yansa/jikokinsa suna da, muhimmiyar rawa a cigaban ruhaniya na ɗan adam. Mafi sanannun addinan Ibrahim sune Yahudanci, Kiristanci da Islama. Ƙananan al'adun addini wasu lokuta ana haɗa su kamar addinan Ibrahim sune Samariyawa, Druze, Rastafari, Yazidi, Babism da Bahá'í. Addinin Mandeniya (addinin da ke riƙe da imanin Ibrahim da yawa) ba a kira shi Ibrahim saboda mabiyansa suna tunanin Ibrahim annabin ƙarya ne.
Addinan Ibrahim na gaskiya suna da tauhidi (imani cewa akwai Allah ɗaya). Sun kuma yi imani cewa ya kamata mutane su yi addu'a ga Allah kuma su yawaita bauta wa Allah. Daga cikin addinan tauhidi, addinin Annabi Ibrahim yana da mabiya mafi girma a duniya. Su ma duk da'a addinan tauhidi. Wannan yana nufin suna da dokoki waɗanda dole ne su bi.