Alqur'ani mai girma

Alqur'ani mai girma
Asali
Shekarar ƙirƙira 631
Asalin suna القرآن‎
haɗawa a Makkah da Madinah
Characteristics
Genre (en) Fassara religious literature (en) Fassara da religious text (en) Fassara
Harshe Ingantaccen larabci
Kintato
Narrative location (en) Fassara Yankin Larabawa
Chronology (en) Fassara

Injil (en) Fassara Alqur'ani mai girma
masu karatun alqur'ani mai girma
Al-Qur'ani
Khatam Al-Qur'an di Bulan Ramadhan.

Al-Qur'ani[1]

rubutun cikin alkur ani
bangon Alkur ani

(Larabci: القرآن al-Qur'an), ko kuma Alƙur'ani mai girma kamar yanda akasani, shine littafin da Allah ya saukar a harshen Annabin Rahama, wato Larabci, kuma shine littafin da Allah ya rufe saukar da duk wani littafi mai tsarki a bayansa, (babu littafin da Allah zai sake saukarwa a bayansa) kamar yadda Allah ya saukar ga Annabawan da suka gabata, domin Annabi Muhammadu shine cika makin Annabawan Allah.[2]

Surat al-Nisa'

Wanda Allah ya saukar da ayoyinsa ga Annabin musulunci Annabi Muhammad (S.A.W) ta hannun mala'ika Jibrilu. A cikin aƙidar Musulunci, Ƙur'ani shi ne mafi muhimmanci kuma mafi girman mu'ujizar Annabi Muhammad (S.A.W), yana tabbatar da cewa Annabi Muhammad (S.A.W) Manzone na gaskiya.[3]

Shari'ar Musulunci, wacce kuma ake kira sharia, ta dogara ne akan Ƙur'ani (Madogararsa na Farko), shine littafin da musulmai suke karantawa, kuma suke aiki dashi, tare da hadisai Waɗanda suke sune maganar da fito daga harshen Annabi Muhammad. Musulmai suna karanta ayoyin kur'ani daban-daban a cikin addu'o'insu.[4]

Lafiyayyan hankali da tsaftataccen tunani na ɗan Adam da ayyuka na yau da kullum sun tabbatar da cewa kur'ani ya bada cikakkiyar kulawa da kariya ta fuskar haƙƙin ɗan adam na duniya, da 'yancin ɗan adam.[5]

  1. https://en.wikipedia.orgview_html.php?sq=engine&lang=ha&q=Quran
  2. https://en.wikipedia.orgview_html.php?sq=engine&lang=ha&q=Al-Tabari
  3. dictionary.reference.com: koran
  4. Bell, Richard; Watt, William Montgomery (1970). Bell's introduction to the Qurʼān. Edinburgh University Press. ISBN 978-0-7486-0597-2.
  5. https://www.iusinitinere.it/clash-between-sharia-law-and-human-rights-in-light-of-pace-resolution-2253-23827

Developed by StudentB