Bauchi | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Suna saboda | Bauchi | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Bauchi | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 6,834,314 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 149.1 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 45,837 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Jihar Arewa maso Gabas | ||||
Ƙirƙira | 3 ga Faburairu, 1976 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | executive council of Bauchi State (en) | ||||
Gangar majalisa | Majalisar Dokokin Jihar Bauchi | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Lambar aika saƙo | 740001 | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | +234 | ||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-BA | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | bauchistate.gov.ng | ||||
Jihar Bauchi jiha ce da ke Arewa maso gabashin kasar Najeriya.Ta hada iyaka daga arewa da Kano da Jigawa,Jihar Taraba da Plateau daga kudu, Gombe da Yobe daga Gabas, sai kuma Kaduna daga Yamma. Jihar ta samo asalin sunanta ne daga tarihin masarautar Bauchi, wacce itace babban birnin jihar a yau. An kafa Jihar Bauchi a shekarar alif dari tara da saba'in da shida (1976), a yayin da aka rarraba tsohuwar Jihar Arewa maso Gabacin Najeriya. A baya Jihar Bauchi ta mamaye yankin Jihar Gombe, wacce daga bisani ta zamo jiha mai zaman kanta a shekara ta alif 1996.[1]
Bauchi itace jiha ta biyar a fadin kasa[2], kuma ta bakwai a yawan jama'a[3]. Ta na da yawan fili kimanin kilomita dubu ar,ba’in da biyar da dari takwas da casa'in da uku (45, 893) da yawan mutane kimanin miliyan bakwai da dubu dari biyar da arba'in da dari shida da sittin da uku (7,540,663)[4] a bisa kidayar shekara ta dubu biyu da shida 2006. Jihar ta rabu dangane da yanayin kasa zuwa kashi biyu (2), West Sudanian savanna daga kudu da kuma semi-desert sahel Savanna daga arewa, da kuma montane Jos Plateau daga kudu maso yammacin Jihar.[5] Daga cikin kayatattun wurare a garin sun hada da, Yankari National Park, wani katafaren wajen ajiye dabbobi ne dake kudancin jihar Bauchi inda akwai dabbobi kaman bijimai, birrai, barewa, zakuna, giwaye da dai sauransu.[6]
Bauchi ne babban birnin jihar Bauchi. Bala Abdulkadir Mohammed shi ne Gwamnan jihar tun zaben shekara ta 2019 har zuwa yau. Wasu daga cikin dattijan Jihar sun hada da: Abubakar Tafawa Balewa, Isa Yuguda, Isah Hamma Misau, Nazif Gamawa, Haruna Ningi da Ali Wakili.
Akwai yaruka da dama a yankuna daban daban na Jihar wadanda suka hada da: Yaren Bolewa, Butawa, da Yaren Warji daga yankunan tsakiyar jihar; Yaren Fulfulde, Yaren Kanuri, da Yaren Karai-Karai daga arewacin garin; Fulani da Yaren Gerawa acikin birnin Bauchi da kewayen ta; Yaren Zaar (Sayawa) daga kudu; Yaren Tangale daga kudu maso gabas; da kuma Jarawa daga kudu maso yamma. Mafi akasarin mutanen gari (kaso tamanin da biyar 85%) musulmai ne, da karamin kaso kiristoci da kaso shida 6% da maguzawa da kaso tara 9%.[7]
A farkon shekarun alif dubu da dari takwas 1800s, Fulani Jihadi sun kwace mafi akasarin garin birnin Bauchi na yau, sannan suka kafa Masarautar Bauchi a karkashin Daular Masarautar Musulunci na Sokoto. A karni na dubu daya da shatara 1900 ne Turawan mulkin mallaka suka mamaye Masarautar kuma suka hade ta a cikin Yankin Mulkin Mallaka na Arewacin Najeriya wacce daga bisani ta zamo Najeriya karkashin mulkin Turawa, kafin samun 'yanci a shekarar alif dari Tara da sittin 1960. Tun asali, yankin Jihar Bauchi a yau tana cikin Yankin Arewa bayan samun 'yanci har zuwa shekarar alif ta 1967 lokacin da aka raba yankin kuma jihar ta fada karkashin Jihar Arewa ta Gabas.[8] Bayan rarraba Jihar Arewa ta Gabas, an kafa Jihar Bauchi a ranar uku 3 ga watan Fabrairu shekara ta dubu daya da dari tara da saba'in da shida 1976 tare da sauran jihohi goma. Shekaru ashirin (20) kuma bayan kafata, an hade wasu kananan hukumomi daga yammacin Jihar inda suka samar da Jihar Gombe.
A matsayinta na jihar da ta dogara da noma, tattalin arzkin Jihar sun ta'allaka ne akan dabbobi da hatsi, kamansu auduga, gyaɗa, dawa, tumatiri da kuma doya tare da cigaba a fannin noman rani na kara habaka samar da abinci tun zamanta jiha. Sannan akwai masana'antu na sarrafa abinci da masana'antun sarrafa kayan abinci na gwan-gwani, da kuma hako ma'adanai kamar tin da columbite, da kuma wuraren bude idanu kamar Dajin shakatawa na Yankari da koramunta na Wikki Springs.[9]