Buddha | |
---|---|
Founded | unknown value |
Mai kafa gindi | Gautama Buddha |
Classification |
|
Practiced by | Buddhist (en) da saṅgha (en) |
Branches | school of Buddhism (en) |
Buddha addini ne wanda ya samo asali daga Indiya, bisa koyarwar Siddhartha Gautama, wanda daga baya ake kira Gautama Buddha. Buddha shi ne wanda aka ce ya farka zuwa gaskiyar rayuwa.
A cikin karnoninsa koyarwarsa ta bazu daga Nepal zuwa Asiya ta Tsakiya, Tibet, Sri Lanka, kudu maso gabashin Asiya, Sin, Mongolia, Koriya, Japan, da yanzu Turai da Arewa da Kudancin Amurka. Addinin Buddha mabiya ɗariƙar Theravada yafi yawa a Kudancin Asiya; Mahayana ya kara arewa. Addinin Buddha ya wanzu a cikin ɓangarori daban-daban a yau, to amma duk makarantu da ƙungiyoyi suna da ra'ayoyi na yau da kuma kullum. Kimanin kashi bakwai cikin ɗari na mutanen duniya mabiya addinin Buddha ne.
Duk da yake mutane da yawa suna ganin addinin Buddha a matsayin addini, [1] wasu suna ganinsa a matsayin falsafa, wasu kuma a matsayin hanyar gano gaskiya . [2] [3]