Gombe | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Suna saboda | Gombe, | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Gombe, | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 3,256,962 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 173.54 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 18,768 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Jihar Bauchi | ||||
Ƙirƙira | 1 Oktoba 1996 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | executive council of Gombe State (en) | ||||
Gangar majalisa | Gombe State House of Assembly (en) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-GO | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | mof.gm.gov.ng |
Gombe jiha ce dake Arewa maso Gabashin Najeriya. Tayi iyaka daga Arewa da Arewa maso gabas da jihohin Borno da Yobe, daga Kudu kuwa da Jihar Taraba, daga Kudu maso yamma kuwa da Jihar Adamawa sannan daga Yamma da Jihar Bauchi. Ta samo asalin sunanta daga babban birninta kuma yanki mafi girma a jihar wato Babban Birnin Gombe - kuma an ƙirƙireta ne daga sashin Jihar Bauchi a ranar daya ga watan Oktoba shekara ta alif dubu daya da ɗari tara da cassa'in da shida 1996. Jihar na daga cikin jihohin da ke ɗauke da ƙabilu iri-iri a Najeriya. Acikin jihohi talatian da shifa 36, da Abuja na Najeriya, Jihar Gombe itace Jiha ta ashirin da daya 21, a girma, kuma ita ce ta talatin da biyu 32, a yawan jama'a, da mutane aƙalla ya kai kimanian miliyan uku da dugo ashirin da biyar 3.25, dangane da ƙiyasin shekara ta dubu biyu da sha shida 2016.[1]
Ta fuskar yanayin ƙasa, Jihar tana da ƙasa nau'in wuraren zafi a yammacin Sudanian Savanna. Muhimman wurare a jihar sun haɗa Kogin Gongola, wanda ke kwarara ta arewaci da Gabashin Gombe zuwa cikin tafkin Dadin Kowa Dam zuwa gaɓar Tsaunukan Muri da ke can yankin kudancin jihar. Daga cikin dabbobi asali na jihar akwai nau'in macizai addun su: carpet viper, puff adder, da kuma Egyptian cobra da kuma dabbobi irin su dorinar ruwa, Senegal parrot, da kuma grey-headed kingfisher.
Jihar Gombe na ɗauke da ƙabilu da dama, yayinda Ƙabilar Fulani suka mamaye yankin arewaci da tsakiyar jihar tare da Bolewa, Kanuri, da kuma Hausawa. A yayin ƙabilu irin su Cham, Dadiya, Jaranci da Kamo, Pero, Tangavle, Tera, da kuma mutanen Waja da suka mamaye yankunan gabashi da kudancin jihar.
Kafin zuwan Turawa, yankin Jihar Gombe ta yau tana ɗauke da ƙasashe da dama masu zaman kansu, har zuwa farkon karni na dubu daya da dari takwas 1800, lokacin da Fulani suka ƙwace yankuna da dama na yankin kuma suka haɗeta a matsayin Masarautar Gombe a ƙarƙashin Daular Sokoto. A cikin karni na dubu daya da dari tara1900, Turawan mulkin mallaka suka mamaye masarautar da yankunan gefen ta kuma sun haɗeta acikin Yankin Mulkin Mallaka na Arewacin Najeriya, inda daga bayan zuwan turawa Nigeria, daga bisani ta samu 'yancin kai a shekarar dubu daya da dari tara da sittin 1960, kuma ta zamo ƙasa Najeriya. Bayan samun 'yancin kai kuwa, Jihar Gombe ta yau ta faɗa ƙarƙashin Arewacin Najeriya har zuwa shekarar dubu daya da dari tara da sittin da bakwai 1967, lokacin da aka raba yankin kuma jihar ta faɗa ƙarƙashin Jihar Arewa ta Gabas. Bayan an raba Jihar Arewa maso Gabas, an ƙirƙiri Jihar Bauchi a shekarar dubu daya da dari tara da saba'in da bakwai 1976, tare da Sauran jihohi guda goma. Shekaru ashirin bayan haka (1996), an cire wasu gungun ƙananan hukumomi daga yammacin Jihar Bauchi don samar da Jihar Gombe.
Dangane da fannin tattalin arziƙi, Jihar Gombe ta dogara ne akan noma da kiwo, da man fetur, inda ake shuka gero, masara, gyaɗa, dawa da tumatiri tare da kiwon dabbobi kamarsu raƙumma, shanu, akuyoyi da kuma tumaki. Sauran muhimman masana'antu sun haɗa da hidindimu na zamani da ake gudanarwa musamman a birnin Gombe. Jihar Gombe itace jiha ta huɗu a jerin ƙarancin Cigaban al'umma.
Tana da yawan fili kimanin kilomita murabba’i 18,768, da yawan jama’a miliyan biyu da dubu uku da hamsin da uku (ƙidayar yawan jama'a shekara ta dubu biyu da shida 2006). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Gombe. Muhammad
Inuwa Yahaya [1] shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta dubu biyu da sha biyar 2015, har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Dr Manasa Daniel Jatau. Dattijan jihar su ne: Sarakunan gargajiya, Malaman addini da kuma jigogin siyasa.[2]