John Adams, Jr. (an haife shi a ranar 30 ga watan Oktoba, shekarar ta alib 1735 -ya mutu a ranar 4 ga watan Yuli, shekara ta ta alib 1826) shi ne Shugaban Amurka na biyu (1797-1801), kuma uba ga Shugaban na shida, John Quincy Adams . Ya kuma kasance Mataimakin Shugaban Amurka na farko (1789–1797).
An haifi Adams a Braintree, Massachusetts . Shi ɗa ne ga Laftanar Col. John Adams, Sr. (1691-1761) da Susanna Boylston (1708-1797), kuma ya kasance ɗan uwan Falsafa Samuel Adams . Ya tafi Harvard College . Ya auri Abigail Adams a cikin shekara ta alib 1764.