Birnin Kairo, da turanci Cairo, Larabci Alqahira. Birni ne dake a lardin Kairo, a ƙasar Misra. Shi ne babban birnin ƙasar Misra kuma babban birnin lardin Kairo. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2010, akwai jimilar mutane 20,439,541 (miliyan ashirin da dubu dari huɗu da talatin da tara da ɗari biyar da arba'in da ɗaya). An gina birnin Kairo a ƙarni na goma bayan haihuwar annabi Isa (AS).