Kano | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Jiha | jihar Kano | ||||
Babban birnin | |||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 3,848,885 (2007) | ||||
• Yawan mutane | 7,713.2 mazaunan/km² | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 499 km² | ||||
Altitude (en) | 488 m | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Lambar aika saƙo | 700001 | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Kano na ɗaya daga cikin manyan birane a ƙasar Hausa. Kano ita ce cibiyar kasuwanci ta Najeriya gaba ɗaya. Jihar Kano tana da ƙananan hukumomi guda arba'in da huɗu.[1] Kano gari ne da yake da masarauta mai ɗunbun tarihi, mai kwarjini a cikin ƙasashen Hausa da kewaye. Haka kuma Kano gari ne babba wanda mazauna cikin sa ke magana da harshen Hausa. Kano ita ce gari mafi yawan jama'a a Najeriya gaba ɗaya.Yaren daya Sahara a duniya gaba daya. Cikin birnin Kano akwai ƙofofi kamar haka Kofar Gadon Kaya, Kofar Famfo, Kofar Na'isa, Kofar nasarawa, Sabuwar Kofa, Kofar Mazugal, Kofar Dawanau, Kofar Dan Agundi, Kofar Dukawuya, Kofar Ruwa, Kofar Kansakali, Kofar Mata.
Yawan mutanen da suke garin Kano ya haura kimanin mutane miliyan goma (10,000,000) a ƙidayar da aka yi a shekara ta alif dubu biyu da shida (2006). Jihar Kano tana da matukar[2] tasiri a yawan mutane a Najeriya, saboda ita ce ta fi kowace jiha yawan mutane a Najeriya. Idan ka zo Kano za ka samu mutane daga ko'ina a fadin duniya, tun daga na kudancin Najeriya, zuwa kasashen dake makwabtaka da Najeriya, haka kuma za ka tarar da mutanen Sin (wato China), da kuma na kasashen Larabawa har da turawan yammacin duniya. Mutanen kano sun shahara wajen ilimin addini sosai.
Kano ta yi suna wajen kasuwancin da ta bunƙasa a kai, har ya zamana ana cewa da ita Cibiyar Kasuwanci. Haka kuma, tarihin Kano ya nuna daman can Kano tana da suna wurin cinikayya tsakaninta da mutanen gabas ta tsakiya.