Kogin Lukenie | |
---|---|
General information | |
Labarin ƙasa | |
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa | 2°43′51″S 18°09′20″E / 2.73089°S 18.15563°E |
Kasa | Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango |
Territory | Bandundu Province (en) |
Hydrography (en) | |
Ruwan ruwa | Kongo Basin |
River mouth (en) | Kogin Fimi |
Kogin Lukenie ( Faransanci : Rivière Lukenie ) kogi ne da ke tsakiyar Kongo na Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo (DRC).
Ruwan fara daga Kinshasa ya haura har zuwa Kongo, Kwah (Kasai), da Kogin Fimi zuwa Lukenie har zuwa Kole, tafiyar na makonni 6 ne zuwa 12. Ba a yin tafiya a lokacin ƙarancin ruwa (Yuni-Agusta), duk da haka, saboda tsoron tsinkewa na dogon lokaci. Ba a iya kewaya Kogin Lukenie ta jirgin ruwa ta yankin Kole.
A farkon lokacin mulkin mallaka na Belgium,wani lokaci ana amfani da kogin don jigilar roba daga tudu irin su Kole da Lodja zuwa tafkin Leopold II. Duk da haka, an kawo mafi yawan kayayyaki daga Bene Dibele, zuwa kudu a gefen dama na kogin Sankuru kusa da wurin da kogin Lubefu ya hade da shi, hanyarsa ya fi aminci.[1]
Wasu daga cikin manyan wuraren yanka katakai na Sodefor suna gefen biyu na Kogin Lukenie, wanda ke kan Oshwe.[2] A watan Satumba na 2010 daruruwan mutane a Oshwe, al'umma a lardin Mai-Ndombe, sun yi zanga-zangar adawa da SODEFOR. Sun bukaci a dakatar da aikin sare itace a yankin, wanda ke lalata dazuzzukan da al’umma ke dogaro da shi ba tare da kawo wani abu da zai rage radadi ga al’ummar da ke fama da talauci.[3]