Komfuta

Komfuta

Kwamfuta na’ura ce mai aiki da wutan lantarki, da ƙwaƙwalwa, wajen karɓa da sarrafawa da adanawa da kuma miƙa bayanai, a sigogi daban-daban. Wannan shine ta’arifin kwamfuta a takaice. Bayan haka kwamfuta na tattare ne da manyan ɓangarori guda biyu; ɓangaren gangan jiki, wanda aka fi sani da Hardware, a turance. Sai kuma ɓangaren ruhi ko rai, wanda ake kira Software (manhaja), shima a turance. Kafin mu yi nisa, mai karatu zai ji ana fassara kalmomin turancin nan, saɓanin yadda zai gamsu ko yake ganinsu a cikin ƙamus (Dictionary). Hakan kuma ya faru ne saboda a yanzu muna cikin wani zamani ne mai suna “turban masana”, ko Information Highway, kamar yadda bayani ya gabata a ƙasidar Matambayi ba ya ɓata. A wannan zamani, kalmomin harsunan duniya za su yi ta sauyawa ne iya gwargwadon fannin ilimi ko rayuwar da ake amfani da su. Don haka sai a kiyaye.[1]

  1. https://en.m.wikipedia.orgview_html.php?sq=albert einstein&lang=ha&q=Computer

Developed by StudentB