Rano | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | jihar Kano | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 520 km² | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
a
Rano ƙaramar hukuma ce kuma hedikwatar masarautar Rano a jihar Kano, Najeriya. mai hedikwatar gudanarwa a cikin garin Rano. Ƙaramar hukumar Rano al'ummar Hausa-Fulani ce dake yankin kudancin jihar Kano wadda aka fi sani da Sanatan Kano ta Kudu tare da Albasu, Bebeji, Bunkure, Doguwa, Gaya, Kiru, Takai, Ajingi, Rogo, Kibiya, Tudun Wada, Garko., Wudil da kuma kananan hukumomin Sumaila. Ƙaramar hukumar Rano kuma ta kafa mazabar tarayya tare da kananan hukumomin Bunkure da Kibiya. Yana da yanki 520 km2 da yawan jama'a 145,439 a ƙidayar shekarar 2006. Ƙaramar hukumar tana iyaka da arewa da kananan hukumomin Garun Mallam da Bunkure, daga gabas da ƙaramar hukumar Kibiya, daga kudu kuma karamar hukumar Tudun Wada, daga yamma kuma ƙaramar hukumar Bebeji. Ƙaramar hukumar Rano ita ce ke kula da harkokin gwamnati a ƙaramar hukumar Rano. Majalisar tana ƙarƙashin jagorancin shugaba ne wanda shine shugaban zartarwa na ƙaramar hukumar. Majalisar dokokin Rano ta kafa dokoki da ke tafiyar da karamar hukumar Rano. Ya kunshi Kansiloli 10 da ke wakiltar unguwanni 10 na ƙaramar hukumar.
Gundumomi 10 da ke ƙaramar hukumar Rano su ne: Dawaki, Lausu, Madachi, Rano, Rurum Sabon Gari, Rurum Tsohon Gari, Saji, Yalwa, Zinyau, Zurgu.
Lambar gidan waya na yankin ita ce 710101.[1]