Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Daular Rumawa wadda a turance ake kira da “Rome” wani ci gaba ne da ya fara bayan wasu kauyuka na kabilun Latin da suka kafu a bakin kogin Tiber (Tiber river ) daga bisani suka hade guri guda inda suka zama birnin Rum a wajejen shekara ta 700 bayan annabi isa al-Masihu. Wanda wannan ne kuma ya kafa tushen kasantuwar Daular Rum.
Masana tarihi sun tabbatar da cewa Daular Rumawa ce mafi girma da kasaita a tsakanin sauran Dauloli da aka samu a zamanin baya. Saboda a lokacin kasaitar ta, Daular Rum ta mallaki babban fadin kasa wanda ya hada da kusan gaba dayan nahiyar Turai (Europe ), yammacin nahiyar Asia, da kuma daukacin arewacin Africa. Haka kuma, tarihi ya nuna cewa Daular Rumawa ta bar wasu muhimman abubuwa wanda duniyar yanzu take cin gajiyar su.