Teku | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | water area (en) , marine water body (en) da saline water body (en) |
Produced sound (en) | Q110068397 |
Nada jerin | list of seas (en) |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Teku wani ginshikin bigire ne, wanda Allahu (SWT) ya gina, sashi ne wanda ya kunshi duniyar ruwa da yake gudana a doron kasa. Teku ne ma'ajiyar duk wani ruwa da yake gangarowa ta'kowanne bangare a fadin duniya.
Kodayake teku ta rabu gida-gida wato kananan teku zuwa kuma manya , kamar irin su tekun atlantika wato "Atlantic Ocean" da kuma tekun maliya wato "Red sea" kasancewar teku nan ne matattarar duk wani ruwa, ta kunshi manya-manyan halittun ruwa kama tun daga kifi, kada, zuwa wasu halittu na daban wadanda ba mu san su ba. Bayan haka dandanon ruwan teku ya kasance mai gishiri-gishiri ne ba kamar yadda ruwan rijiya yake ba.
Masana ilimin kimiyya sun tabbatar da cewa inda ruwa ya mamaye ya fi inda kasa ta mamaye. A bisa kididdiga kuma inda ruwa ya mamaye ya kai kashi saba'in da biyar cikin dari (75%), amma inda kasa ta mamaye kwata-kwata kashi ashirin da biyar ne cikin dari (25%).