Google babban kamfani ne dake ƙasar Amurka. An san shi ne don ƙirƙira da gudanarwar ɗayan manyan injunan bincike na yanar gizo na Duniya "(WWW)" ma'ana (("World" "Wide""Web")), Kowace rana fiye da mutane biliyan suna amfani da shi. Hedikwatar Google (wanda aka fi sani da" Googleplex ") yana cikin Mountain View,California, wani ɓangare na Kwarin Silicon.Taken Google a halin yanzu shi ne "A yi abin da ya dace". Tun daga ranar 2 ga Satumbar 2015, Google mallakar wani sabon kamfani ne mai suna Alphabet Inc, wanda ya karbe wasu ayyukan na Google, kamar motocinsa marasa matuƙi.Kamfani ne na jama'a da ke kasuwanci a kan NASDAQ ƙarƙashin tambarin GOOG da GOOGL. Injin bincike na Google na iya nemo hotuna, bidiyo, labarai, rukunin labarai na Usenet, da abubuwan da za a saya ta kan layi Zuwa watan Yunin 2004,Google yana da shafukan yanar gizo biliyan 4.28 a kan rumbun adana bayanansa, da hotuna miliyan 880 da sakonnin Usenet miliyan 845 - abubuwa biliyan shida. Gidan yanar gizon Amurka na Google yana da matsayin Alexa na 1, ma'ana shine gidan yanar gizon da akafi ziyarta a duniya.Sanannen abu ne cewa wasu lokuta mutane suna amfani da kalmar "[ https://simple.wiktionary.org/wiki/google google]" a matsayin fi'ili da ke nufin "neman wani abu a Google";amma saboda sama da rabin mutanen da ke yanar gizo suna amfani da shi,"google" an yi amfani da shi wajen "bincika yanar gizo".